Saturday 29 November 2025 - 13:08
An gudanar da taron ranakun Faatimiyya a birin Nawakishot na ƙasar Muritaniya

A yankin Nawakishot, babban birnin ƙasar Muritaniya, an gudanar da taron ranakun Fatimiyya tare da halartar mabiya da masu ƙaunar Ahlul Baiti (AS).

A cewar rahoton sashen fassara na ofishin dillancin labaran Hawza, a Nawakishot, babban birnin Muritaniya, a lokacin taron shekara-shekara na shahadar Sayyida Fatima Zahra (SA), an gudanar da wani gagarumin taron jaje wanda mabiya da masoyan Ahlul Bayt (AS) suka halarta. Wannan taron na ibada an fara ne da karatun ayoyin Alƙur'ani mai girma, wanda ya ƙawata yanayin majalisin da ƙamshin kalmomin Allah.

A ci gaba da taron, Sheikh  Muhammad Fal a cikin jawabinsa ya jaddada wajibcin bin Ahlul Baiti (AS), inda ya siffanta su da "taurarin shiriya" ga al'ummar Musulmi. Ya kuma yi nuni ga koyarwar Alƙur'ani da Sunnar Manzon Allah, kan jaddada wajibcin nisantar kafirai da munafukai a matsayin ɗaya daga cikin ka'idojin makarantar Ahlul Baiti. Ya ce, riƙo da wilaya da nisantar maƙiyan gaskiya, shine sirrin dorewa da haɓakar al'ummar Musulmi a fannin ruhaniya.

A ci gaba da jawabinsa, ya yi karin haske game da zaluncin da aka yi wa Sayyida Zahra (AS), tare da bayyana matsayinta, halinta da kuma iliminta. Ya bayyana jigon huduba "Fadakiyya" a matsayin wata babbar alama da take nuna tsananin fasaha da iliminta. Ya kuma ɗauki wannan huduba a matsayin shaida mai ɗorewa wajen kare wilaya da wayar da kan al'umma.

A ɓangaren ƙarshe na taron, an karanta ziyarar Sayyida Faatima Zahra (AS). An karkare taron da tunawa da sunan wannan babbar uwargida ta sama da kasa da kuma ba da shawarwari a kan ɗabi'a da ibada. Wannan taro ya sake nuna wani abin al'ajabi na zurfin ƙaunar Musulmin Muritaniya ga gidan Annabta (AS).

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha